Ya bayyana Takutaha a matsayin wata muhimmiyar dama da ke tunatar da al’ummar Musulmi game da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) a watan Rabi’ul Awwal.
A cewarsa, ya kamata bikin ya zama lokaci na yin tunani a kan rayuwar Annabi (SAW), koyarwarsa da kyawawan ɗabi’un da ya yi wa al’umma jagora a kansu, musamman zaman lafiya, tausayi, adalci, haɗin kai da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma.
Gwarzo, wanda aka fi sani da Jagoran Amana, ya yi kira ga Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen sabunta imaninsu, ƙarfafa zumunci da ’yan uwantaka, tare da yaɗa haƙuri, fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Haka kuma, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su ƙara yawan addu’o’i ga al’ummomin da matsalar rashin tsaro ta shafa, musamman yankunan da ke kan iyaka da wasu ƙananan hukumomin jihar.
Ya jaddada cewa samun zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin kan al’umma da kuma ci gaba da yin addu’o’i.
Ɗan takarar gwamnan na NDC ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su riƙe kyawawan ɗabi’un soyayya, adalci, zaman lafiya da mutunta juna, waɗanda ya ce suna daga cikin muhimman koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Gwarzo ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya, ci gaba da wadata ga Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya, tare da kira ga Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun daidaito da ci gaban ƙasar.
Ya kuma sake tabbatar wa al’ummar Kano da cewa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a zaɓen 2027, zai mayar da hankali wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci, riƙon amana, haɗin kai da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Tushen Labari: KADAURA24