Atiku Ya Ce Zai Yafe Wa Ɗalibai Bashin NELFUND Idan Ya Ci Zaɓe

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin sake nazarin tsarin Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) tare da yi wa wasu ɗalibai afuwa kan bashin da ake bin su idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

 

Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Jama’a, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, yayin da yake mayar da martani kan kalaman Shugaba Bola Tinubu game da tattalin arziƙi da tsarin lamunin ɗalibai.

 

Tinubu ya ambaci NELFUND a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani kan wasu shawarwarin da Atiku ya bayar kan tattalin arziƙi, ciki har da shirin rage tsadar makamashi.

Sai dai Shaibu ya soki yadda shugaban ƙasar ya gabatar da NELFUND a matsayin wata shaida cewa ilimi ya zama abu mai sauƙi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

 

Ya ce gwamnati ta taimaka wajen ƙara tsadar ilimi kafin daga bisani ta samar da lamuni domin taimaka wa ɗalibai su iya biyan kuɗaɗen karatu.

Shaibu ya ce ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen rage tsadar ilimi maimakon tilasta wa ɗalibai cin bashi.

 

Ya ce idan Atiku ya zama shugaban ƙasa, zai sake duba tsarin lamunin tare da yi wa wasu ɗaliban da suka cancanta afuwa.

 

“Ya kamata ilimi ya buɗe wa mutum ƙofa, ba ya tare masa makomarsa ba,” in ji Shaibu.

 

Ya ƙara da cewa bai kamata a ɗauki lamunin ɗalibai a matsayin tallafin karatu ba.

 

Ya ce nasarar manufofin ilimi ya kamata ta kasance wajen tabbatar da cewa iyalai masu ƙaramin ƙarfi za su iya tura ‘ya’yansu makaranta ba tare da cin bashi ba.

 

Shaibu ya kuma yi watsi da iƙirarin cewa shirin Atiku na rage tsadar makamashi zai iya shafar kuɗaɗen NELFUND, albashin ma’aikata ko mafi ƙarancin albashi.

 

Ya ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana yadda shirin Atiku, wanda ya shafi ɗanyen man Nijeriya da ake samarwa domin tacewa a cikin gida, zai rage kuɗaɗen da ake ware wa ɗalibai da ma’aikata.

 

A cewarsa, rage farashin makamashi da sufuri zai taimaka wajen ƙara darajar albashin ma’aikata tare da rage matsin tattalin arziƙi da ke kan ɗalibai da iyayensu.

 

Shaibu ya ce shirin Atiku zai mayar da hankali ne wajen rage tsadar ilimi da rayuwa, maimakon dogaro da bashi domin taimaka wa ‘yan Nijeriya su shawo kan tsadar rayuwa.

 

MAJIYA: Leadership Hausa.