Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan ta’adda biyu yayin wani samame da suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
An gudanar da samamen ne a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, a kusa da ƙauyen Kogo, bayan sojoji sun samu bayanan cewa wani ƙasurgumin shugaban ’yan ta’adda, Kachalla Muhammadu Filani, da mambobin ƙungiyarsa suka ɓuya a yankin.
Sojojin sun bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan, inda suka yi musayar wuta da su tare da kashe wasu manyan kwamandojinsu biyu.
Waɗanda aka kashe sun haɗa da Hamisu, wanda aka fi sani da MAMIYO, wanda ake zargi da safarar makamai kuma shi ne mataimakin Kachalla Muhammadu Filani, da kuma Umar Bocho, wanda shi ma babban jagora ne a ƙungiyar.
Sai dai Kachalla Muhammadu Filani ya tsere daga wurin arangamar da raunukan harbin bindiga a jikinsa.
Sojoji sun ce suna ci gaba da nemansa.
Rundunar ta ce kashe kwamandojin biyu zai raunana ƙungiyar tare da kawo cikas ga ayyukanta a yankin.
Sojojin sun ci gaba da gudanar da ayyuka domin gano inda Filani yake tare da kawar da sauran barazanar tsaro a yankin.
MAJIYA: Leadership Hausa.